Daga Comr Abba Sani Pantami
Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Muhammed, ta dage cewa dole ne a yi adalci kan kisan Deborah Samuel da aka yi wa kisan gilla, sannan aka kona ta a Sokoto.
Amina Muhammed, wacce ta gabatar da bukatar a yi adalci a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Talata, ta bayyana cewa bai kamata a “karkatar da addini don yin wa’azin tashin hankali ba”.
Sanarwar ta kara da cewa: “Dole ne a yi adalci kan kisan gilla da aka yi wa matashiyar Deborah Yakubu a Najeriya. Bai kamata a yi wa addini mummunar fassara don yin wa’azin tashin hankali ba sa’ad da suke kawo zaman lafiya.