fbpx
Monday, August 15
Shadow

Don Allah kar ku kuje ni kan fadi zaben danayi, gwamnan jihar Osun ya roki membobinsa

Gwamnan Osun dan jam’iyyar APC wanda ya fadi zaben jihar da aka gudanar ranar 16 ga watan Yuli, wato Oyetola ya roki membobinsa cewa kar su guje shi kan fadi zaben daya yi.

Inda kuma yace masu kar su rarraba kawunansu domin har yanzu shine akan mulki kuma zai cigaba da lura da al’amuran jihar.

Inda kuma ya gana da jami’an tsaron jihar yace masu cigaba da aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya a jihar ta Osun.

A karshe gwamnan yace masu zai cigaba da mulkin jihar da zuciya daya duk da ya fadi zabe kuma zai cigaba da kare rayukansu da dukiyoyin su bakidaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.