fbpx
Thursday, June 30
Shadow

“Don Allah ko zabe ni a zaben fidda gwani”>>Bola Ahmad Tinubu ya roki wakilan APC na Jigawa

Tsohon gwamnan jihar Legas dake neman takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC, Tinubu ya roki wakilan jam’iyyar na jihar Jigawa dasu zabe shi a zaben fidda gwani mai zuwa.

Bola Ahmad Tinubu ya kara da cewa ba kowa ne dake neman kujerar shugabancin Najeriya ya cancance ta ba saboda, saboda haka su girmama shi su zabe shi.

Ya bayyana masu hakan ne yayin dayake ganawa dasu a ranar juma’a a babban birnin Jigawa, watau Dutse kuma ya roki gwamnan jihar Muhammad Badaru ya bashi goyon baya domin wakilan jihar su zabe shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.