fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Don Allah ku ceto mana sauran ‘yan uwanmu, iyalan mutanen da aka yi garkuwa dasu a jirgin kasa na jihar Kaduna suka roki gwamnatin tarayya

Iyalan mutanen da aka yin garkuwa dasu a jirgin kasa na jihar Kaduna sun sake kira ga gwamnatin tarayya cewa ta taimaka ta ceto masu sauran ‘yan uwansu.

Inda sukace sunji dadin mutane 11 da gwamnatin ta ceto a kwanakin baya amma suna so a cetosu gabadaya domin hankulansu su kwanta.

Sun bayyana hakan ne a taron da suka gudanar ranar alhamis inda shuwagabanninsu Dr. AbdulFatai Jimoh da Dr. Ba’aba Muhammad sukace ‘yan uwan nasu ba wata cikakkiyar kulawa suke samu a hannun ‘yan bindigar ba.

Karanta wannan  Gabadaya sansanin mu ya cika bamu da wurin ajiye tubabbun 'yan Boko Haram a Borno, cewar Gwamna Zulum

Kuma wasun su zasu fara tunanin kashe kawunansu akan cigaba da zaba tare da miyagun mutanen nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.