fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Don Allah ku ceto sauran mutanen dake hannun ‘yan bindiga domin ba sauki, cewar yaron shugaban dattawan Arewa daya kubuta a hannun ‘yan bindiga

Daya daga cikin mutane bakwai da suka samu ‘yanci a makon daya gabata cikin fasinjojin da ‘yan bindiga sukayi garkuwa dasu a jirgin kasa na jihar Kaduna,

Sadik Ango Abdullahi wanda ya kasance yaron shugaban kungiyar dattawan Arewa ya roki gwamnanatin Najeriya cewa ta ceto sauran mutanen dake dajin domin ba sauki suna shan wahala.

Amma shi yana mika sakon godidayarsa ga daukacin mutanen da suka taya shi da addu’a ya kubuta daga hannun ‘yan bindigar.

Sai dai yace yana jin tausayin sauran yara da kuma tsaffin mutanen daya bari guda 43 a hannun ‘yan bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.