fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Donald Trump ya kori jami’in Gwamnatinsa daga Aiki bayan da yace zaben Gaskiya Akayi a Amurka

Shugaban kasar Amurka,  Donald Trump ya bayyana korar Christopher Krebs wanda shine shugaban hukumar kula da tsaron yanar gizo daga aiki bayan da yace zaben gaskiya aka yi a kasar Amurka.

 

Krebs ya jagoranci wani bincike kan zaben na kasar Amurka da aka yi dan tantance sahihancinsa kuma sakamakon binciken da yayi ya bayyana cewa zaben shine mafi inganci a tarihin kasar.

 

Saidai a Martanin Trump ta shafinsa na Twitter ya bayyana cewa wannan ba gaskiya bane an masa magudi inda har matattu sun yi zabe kuma injinan zabs basu yi aiki da kyau ba inda aka rika baiwa abokin takararsa Joe Biden kuri’u sannan kuma yayi zargin cewa bayan kulle Rumfar Zabe wasu sun rika saka kuri’u.

 

Yace dan haka sakamakon binciken Kreb ba gaskiya bane kuma dalilin haka ya koreshi daga aiki nan take.

Karanta wannan  Yadda hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya cigaba da karbar albashin miliyoyin naira duk da yayi murabus

 

Saidai a martaninsa, Kreb ya bayyana cewa, ba karamar karramawa bace aikin da yayi kuma sun yi abinda ya kamata. Sun gyara yau dan gobe.

The recent statement by Chris Krebs on the security of the 2020 Election was highly inaccurate, in that there were massive improprieties and fraud – including dead people voting, Poll Watchers not allowed into polling locations, “glitches” in the voting machines which changed …votes from Trump to Biden, late voting, and many more.

 

Therefore, effective immediately, Chris Krebs has been terminated as Director of the Cybersecurity and Infrastructure Security Agency.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.