by hutudole
Yayin da Dortmund suka samu damar kasancewa na biyu a gasar Bundlesliga su kuma Haffenheim suke fafitikar neman cancanta a gasar Europa lig, Haffenheim ne suka samu nasara a wasan yayin da Kramaric ya fara cin kwallo a wasan cikin minti na takwas.
Dortmund sun yi kokari sosai kafin aje hutun rabin lokaci yayin da Achraf Hakimi da Jadon Sancho suka kasance a benci su kuma Haffenheim suka kara jefa wata kwallon kuma Kramaric ne ya kara cin kwallon. Amma sai dai Dortmund sun kasa cin kwallon a wasan.

Bayan wasu mintina kuma Kramaric yaci kwallon shi ta uku a wasan. Dortmund sun shigo da Jadon Sancho da Achraf Hakimi bayan an dawo daga hutun rabin lokaci amma duk da haka an cigaba da zira masu kwallayen kuma duk mutun daya ne yaci su.
A karshe dai an tashi wasan 4-0 wanda Dortmund suka yi abin kunya a gidan su su kuma Haffenheim suka samu cancanta a gasar Europa lig na kakar wasan badi. Kramaric ya zamo dan wasan daya ci kwallaye guda hudu a wasa a daya na gasar Bundlesliga a wannan kakar.