fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Dortmund 2-0 RB Leipzig: Haaland yaci kwallaye biyu yayin da Jadon Sancho ya kasance a benci

Erling Braut Haaland yayi nasarar cin kwallaye har guda biyu yayin da suke karawa da kungiyar RB Leipzig dazu. Kuma Dortmund yanzu sun tabbatar da cewa zasu kasance na biyu a gasar Bundlesliga saboda nasarar da suka yi na 2-0.

Dortmund sun sha wahala a hannun kungitar Mainz a tsakiyar wannan makon a gidan su yayin da suka basu kashi har 2-0, kuma suma yanzu Dortmund sun rama abun da aka yi masu yayin da suka karyawa RB Leipzig kokarin da suka yi na buga wasanni 13 ba tare da an cire suba.
Dortmund sun hana Timo Warner cin kwallo a wasan shi na karshe a kungiyar RB Leipzig kafin ya koma Chelsea. Haaland ya kai hari sau biyu amma Gulacsi ya hana shi cin kwallon, kuma shima Thorgan Hazard ya kai hari amma dan wasa ya hana shi cin kwallon.
Dortmund sun yi kokari sosai kafin aje hutun rabin lokaci yayin da Giovanni Reyna ya taimakawa Haaland wajen cin kwallo shi ta farko, kuma Jadon Sancho ya kasance a benci. Haaland yayi nasarar jefa kwallon shi ta biyu bayan an kara masu minti uku yayin aka kusa tashi wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Zamu sayar da kai amma bisa sharadi guda, Manchester United ta fadawa Cristiano Ronaldo

Leave a Reply

Your email address will not be published.