Kaftin din Dortmund, Marco Reus ya taimakawa sabon kocin kungiyar Edin Terzic ya samu nasara a wasa na farko daya fara jagirantar kungiyar, bayan ta kori Lucien Favre sakamakon lallasawar da Stuttgart tayiwa Dortmund 5-1 a gidan ta.
Kungiyar Dortmund ta yiwa Terzic kwantiraki ne izuwa karshen kakar yayin da yayi nasarar jagorantar kungiyar ta samu nasara karo na farko a cikin wasanni hudu data buga na gasar Bundlesliga.
Dortmund ta fara jagorancin wasan ne ta hannun Guerreiro kafin Sergent ya ramawa Bremen kwallon. A karshe dai Dortmund ce tayi nasarar lashe gabadaya maki uku na wasan bayan Reus yayi nasarar ci mata kwallo guda ana daf da tashi wasa.
Sakamakon wasan yasa yanzu Dortmund ta koma ta hudu a saman teburin gasar Bundlesliga yayin da Bayer Leverkusen ta wuce ta da maki biyar a saman teburin gasar.