fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Dortmund 4-0 Freiburg: Jadon Sancho ya kara rasa wasan Dortmund karo na biyu a jere

Tauraron dan wasan Ingila wanda Manchester United take farautar siya a wannan kakar wato Jadon Sancho ya kara rasa wasan Dortmund karo na biyu saboda matsalar numfashi da yake fama da shi.

Dan wasan Amurika mai shekaru 17 Giovanni Reyna shine ya mayewa kungiyar gurbin Sancho a wasan kuma yayi kokari sosai tare da Haaland yayin da suka taimakawa Dortmund tayi nasarar cin hudu bayan ta sha kashi a makon daya gabata.

Dan wasan kasar Norway Haaland yaci kwallaye biyu a wasan yayin da gabadaya kwlayen shi na wannan shekarar suka kama 17 daga wasanni 18 daya buga na Bundlesliga.

Karanta wannan  Mutane 18 sun mutu sakamakon hadarin mota akan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

Emre Can shima yayi nasarar zira kwallo guda a wasan sai kuma ana gab da tashi Haaland ya taimakawa Felix Passlack ya zira kwallo guda wadda ta kasance ta hudu duk da cewa zakaran kungiyar su Sancho bai buga wasan ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.