A ranar lahadi 31 ga watan mayu kungiyar Dortmund suka Kara da Paderburn kuma sunyi nasara a wasa yayin da suka tashi 6-1, kuma Sancho yayi nasarar jefa kwallaye har guda uku a wasan.
Gabadaya kungiyoyin basu ci kwallo ba kafin aje hutun rabin lokaci, bayan an dawo kuma da Hazard shine ya fara cin kwallo bayan minti uku Sancho shima ya jefa kwallo daya. Dan wasan ingilan ya bayyana wata riga wadda aka rubuta “a yiwa George Floyd adalci bayan yaci kwallo shi ta farko a wasan.

Dortmund sun sha gwagwarmaya kafin aje hutun rabin lokaci yayin da tauraron su Haaland bai buga wasan ba saboda yana da rauni. Bayan Dortmund sun ci kwallo biyu, dan wasan Paderburn Hunemeier yaci kwallo daya kuma bayan minti biyu Sancho ya kara cin wata cin wata kwallon.
Yayin da aka kusa gama wasan Achraf yaci kwallo kuma bayan minti uku shima Schmelzer yayi nasarar jefa kwallo daya. Tauraron su Jadon Sancho ya cika kwallon shi ta uku a wasan wadda yayi nasarar jefawa a minti na 91.