Jadon Sancho ya taimaka wurin cin kwallon da Achraf Hakimi yaci bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, yayin da suka dakko shi daga benci a minti 65.

Borussia Dortmund sun samu karin maki yayin da Raphael Guerriero yayi nasarar cin kwallo kafin aje hutun rabin lokaci a minti na 32. Wolfsburg sun kaiwa Dortmund hare-hare da dama amma sai dai basu samu nasarar jefa ko kwallo daya ba.
A karshe Dortmund sum samu karin maki uku yayin da suka kasance bayan zakarun gasar Bayern Munich da maki daya kacal su kuma Wolfsburg suka kasance na shida a teburin gasar.