Hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS ta gargadi shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa tsayar da musulmai duka a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ka iya kawo rikicin addini a kasar.
Hukumar ‘yansandan farin kayan ta fitar da wannan sanarwa ne bisa hadin gwiwar hukumar ‘yansanda ta kasa.
Jam’iyyar APC dai ta tsayar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa a shekarar 2023 sannan shi kuma ya dakko Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.
Kafar Peoplesgazette ta bayyana cewa, an mikawa shugaban kasar da wannan sanarwar ne ta hannun me bashi shawara kan harkokin tsaro watau Babagana Monguno.