Hukumomi a Sudan sun ce dubban tumaki sun mutu a ruwa bayan wani jirgin ruwa ya kife a hanyarsa ta zuwa Saudiyya.
Rahotanni sun ce duka bil’adama da ke cikin jirgin sun tsira. Jirgin dai na ɗauke ne da kusan dabbobi dubu 16.
Jami’an tashar ruwa a Sudan ɗin sun bayyana cewa adadin dabbobin da jirgin ya kwasa ya fi ƙarfin adadin da zai iya ɗauka.
Ana matuƙar buƙatar tumaki a Saudiyya ganin cewa miliyoyin Musulmi za su yi layya a Babbar Sallah mai zuwa.