fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamnatin tarayya tasha al’washin biyan Dubu 20,00 ga matasa marasa aikinyi don share kasuwanni da mugudanai

“Dubu 20,000 zamu ringa biyan matasan da za suna aikin share kasuwanni da magudanai a cewar gwamnatin tarayya tabakin karamin ministan gwadago Festus Keyamo.

A watannin baya gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na daukar matasa 774,000 aiki na wucin gadi wanda zasu yi aiki tsawon watanni 3.

Aikin da matasan zasu yi shine sharar kwatoci da sharar Titi da kuma sharar kasuwa da makarantu.
Idan zaku iya tunawa a wancan lokacin Ministar kudi da kasafin kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmad ta bayyana cewa za’ayi amfani da Biliyan 60 daga kudin tallafin Coronavirus/COVID-19 wajan yin wannan aikin kuma za’a yi aikin daga watannin Octoba zuwa Disamba na shekarar 2020.
Haka zalika Aikin zai fi mayar da hankaline a yankunan karkara kuma ba’a bukatar mutum sai yana da takardar shaidar karatu.
A cewar karamin Ministan kwdago Festus Keyamo (SAN) a lokacin da yake bayyanawa manema labarai wanda jaridar Punch ta rawaito a ranar Alhamis, Festus  ya shaida cewa za’ana biyan Naira dubu 20,000 ga dukkan wanda gwamnati ta dauka aikin share magudanun ruwa da tituna da kasuwanni a kowanne wata.
Ya kara dacewa masu cin gajiyar aikin za’a bude musu asusu a bankuna bugu da kari za’ana  biyan su hakkokin su daga babban bankin kasa izuwa asusun da aka bude musu.

Haka zalika Jihohi 8 da aka fara dasu karkashin hukumar samar da aiki ta kasa,NDE sune Ebonyi, Edo, Katsina,Ekiti, Adamawa, Kwara, Borno, Jigawa.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada Aliko Dangote a matsayin shugaban sabuwar kungiyar da zata kawo karshen cutar Malaria a Najeriya

Haka zalika Aikin za’a farashine bayan damuna inda za’a baiwa matasan da basu da ikin yi dama.

 

Saidai gwamnatin tace a wannan karin an fadada aikin zuwa jihohi 36 na kasarnan. Za’a dauki matasa 1000 daga kowace karamar hukuma 774 ta kasarnan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.