Wani karamin soja ya bayyana cewa akwai yiyuwar yiwa manyan sojoji tawaye idan ba’a saka ido kan yanda suke zaluntar kananan sojoju ba a Najeriya.
Sojan dake aiki a Yola ya bayyana cikin fushi cewa muddin ba’a dauki mataki kan lamarin ba zai kai matsayin da ba za’a iya maganinsa ba.
Sojan yayi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya dauki mataki kan lamarin kamin ya kazance.
Yace ana tirsasa musu sayen kayan aiki akan Naira 42,000.