fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

DUBU TA CIKA: Asirin Wani Da Ya Daɗe Yana Kaiwa Ƴan Bindiga Bayanan Sirri A Jihar Katsina Ya Tonu

Daga Comr Nura Siniya

Kamar yadda kuke gani Shugaban ƙaramar hukumar Jibia ne Hon. Bashir Sabi’u Maitan, ya kama wani mutum da hannun shi mai suna Aminu Gangara da ya shahara wajen bada bayanan sirri ga ƴan bindiga (Informer) wanda ake zargin yana da hannu dumu-dumu a ta’addancin da ake a garin Bugaje da Gangara da kuma garuruwan da suke ƙarƙashin Masarautar Ɗaɗɗara dake Jibia a jihar Katsina

A rahoton da muka samu an zargi Aminu Gangara da kaiwa ƴan bindiga bayanan sirri akan wani Attajirin yankin da barayin dajin suka ɗauka Alhaji Tasiu Waliyi da sauran wasu mutane a yankin.

Karanta wannan  Wani matashi mai samar da waraka daga cutar makanta ya bayyana a fakistan

Muna roƙon Allah ya ƙara tona asirin duk wani mai hannu a cikin taɓarɓarewar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa da Najeriya baki ɗaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.