fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

“Duk da banyi zurfi a karatun boko ba amma hakan bai hana masu digiri da digirgir ba yin aiki a kamfanonina ba”>>inji Atiku yayin da ya mayarwa wani martani daya cemai beyi nisan karatu ba

Kwanan nan ne wani jigo a kasarnan yayi tsokaci akan abinda yake tunanin cewa zai faru a lokacin zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu inda yace yana ganin shugaba Buharine za’a sake zaba ko kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Wannan yasa wani ya kutsa dandalin Atikun na shafin sada zumuna da muhawara na Twitter yake rubuta cewa “Shugaba Buhari bashi da Ilimi, shi kuma Atiku yayi karatu amma sama-sama/ba sosai ba.

Ai kuwa koda Atikun yaga wannan rubutu sai ya mayarwa da mutumin amsar cewa ” Na gode(Allah) masu digirin dacta da suke aiki a kamfanonina rashin karatuna be damesu ba”.
Bayan mayar wa da wannan mutumin amsarnan ne sai wasu da sukayi sharhi akan wannan batu sukata yabon Atikun suna ceqa ya baiwa mutumin amsar data dace.

Koda a watan daya gabata sai da shahararren dan kasuwarnan kuma attajiri watau Muhammad Indimi ya bayyana cewa bai taba yin karatun boko ba, amma masu digiri da digirgir na aiki a karkashinshi .

Leave a Reply

Your email address will not be published.