fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Duk da gargadin da sojoji suka mai, Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa yana nan kan bakansa dole jama’ar jiharsa su dauki makamai dan kare kansu

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa, yana nan kan bakansa na mutanen jiharsa su dauki makamai dan kare kansu.

 

Hakan na zuwane bayan da shugaban sojoji, janar Lucky Irabor yace hakan ya sabawa doka.

 

Gwamnan a jihar tuni ya kaddamar da wani kwamiti da zai kula da kawo karshen matsalar ‘yan Bindiga a jiharsa.

 

Tuni kuma ya baiwa kwamitin mashina da motocin da zasu taimaka musu yin aikinsu.

 

Gwamnan yace amma za’a bi doka wajan baiwa jama’a damar mallakar makaman.

Karanta wannan  Rundumar sojin sama sun hallaka shugaban 'yan ta'addan Boko Haram da tawagarsa a jihar Maiduguri

 

Yace sun dauki wadannan matakai ne saboda sojojin Najariya basu da isassun kayan aikin da zasu iya magance matsalar tsaron da ake fama da ita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.