fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Duk da hanin jami’an tsaro, ‘yan Shi’a sun yi zanga-zanga yau a Kaduna

Mabiya kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Shi’a, IMN sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin Kaduna na jihar Kaduna a yau, Juma’a duk da hanin hukumomi.

 

A baya dai mun kawo muku yanda jami’an taaro suka tarwatsa wani gangamin ‘yan shi’ar a babban birnin tarayya Abuja yayin da suke neman a saki shugabansu, Ibrahim Zakzaky.

Saidai a yau ma ‘yan Shi’an sun sake fitowa Gangami a Kaduna. Da yake magana a lokacin zanga-zangar, Aliyu Tirmizi ya bayyana cewa Duniya ta gani ta kuma yi Allah wadai da kisan da akawa Zakzaky da jama’arsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.