fbpx
Monday, March 1
Shadow

Duk da ikirarin cewa ba’a fahimceshi bane, Muryar Ministan harkokin kasashen Waje ta bayyana yana cewa kasar Benin Republic na son hadewa da Najeriya

Maganar Ministan Harkokin kasashen waje na Najeriya,  Geoffrey Onyeama ta cewa kasar Benin Republic na son hadewa da Najeriya dan zama jiha ta 37 ta jawo cece-kuce.

 

Bayan hakane sai ma’aikatar ta fitar da sanarwar cewa ba’a fahimci Ministan bane ko kuma an canja masa magana.

 

Saidai binciken da aka yi dan gano ainahin abinda ya fada ya bayyana cewa lallai Ministan ya fadi waccan Magana.

 

Daily Trust ta wallafashi yana fadin cewa lallai shugaban kasar Benin Republic Patrice Talon ya bayyanawa shugaba Buhari cewa suna son zama jiha ta 37 a Najeriya kuma ba da wasa suke ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *