Jaridar Forbes me fitar da jadawalin masu kudin Duniya, tace masu kudin Najeriya sun kara kudancewa a shekarar 2022.
Hakan na faruwa ne duk da cewa zuwa cutar coronavirus ya karade Duniya inda aka samu matsin tattalin arziki.
Dangote wanda shine na daya a Africa ya samu karin arziki daga biliyan $11.5 a shekarar 2021 zuwa biliyan $14 a shekarar 2022.
Mike Adenuga kuwa ya samu karin arziki ne daga biliyan $6.1 a shekarar 2021 zuwa Biliyan $7.3 a shekarar 2022.
Shi kuwa Abdulsamad Rabiu ya samu karuwar arziki daga Biliyan $4.9 a shekarar 2021 zuwa Biliyan $6.9 a shekarar 2022.