Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo wanda dan takarar PDP, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe inda ma har ya taya gwamnan murnar lashe zaben.
Hakanam uwar jam’iyyar APC ta kasa ta bakin shugaban ta na Riko, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ta amince da sakamakon inda itama ta taya Gwamna Obaseki murna.
Saidai duk da haka Adams Oshiomhole da Bola Ahmad Tinubu wanda duka sun yi kamfe din kada a zabi Obaseki har yanzu basu ce komai ba.
Rigima da Oshiomhole da Tinubu ta kai ga Oshiomholen ya rasa kujerarsa ta shugaban jam’iyyar APC sannan kuma Obaseki ya bar APC bayan da aka hanashi takarar gwamna a jam’iyyar inda ya koma PDP.
A maganar da yayi da manema labarai, Obaseki ya bayyana Oshiomhole da Tinubu a matsayin wanda suke aikin da baya cikin kundin tsarin Mulki.