fbpx
Monday, August 8
Shadow

Duk gwamnan da bai bude masallatai ba a yanzu son raine kawai>>Sheikh Nura Khalil

Shehin Malamin addinin Islama, Sheikh Nura Khalin yayi nagana akan hana sallah da gwamnatoci suka yi a cikin Najeriya.

 

A tafsirin da yayi wanda wakilinmu ya saurara, Malam ya bayyana cewa ana maganar cewa hana cinkoso a guri daya ne yasa aka hana sallah.

 

Yace to amma me yasa aka kirkiri cinkoso a cikin kasuwannin mu, yace ai kamin zuwan Coronavirus/COVID-19 babu cinkoso a kasuwannin, zaman gida dolene ya kawo cinkoson.

 

Yace duk gwamnan daya ci gaba da hana sallah a yanzu to Son raine kawai, yace a duba wane irin tsarine aka yi a kasar Nijar aka dawo da yin Sallah, wane irin tsarine aka yi a ,Zamfara aka dawo da Sallah sannan wane irin tsarine aka yi a Borno aka dawo da yin Sallah?

Leave a Reply

Your email address will not be published.