Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karyata rade-radin dake yawo cewa wai zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Hakanan maganganun dake yawo sun kuma bayyana cewa, Jonathan din dai koma jam’iyyar APC kamin ya tsaya takarar.
Saidai a nasa martanin ta bakin kakakinsa, Ikechukwu Eze, Jonathan yace ba haka bane.
Yace ko da yawan zuwa wajan shugaba Buhafi da aka ga yanayi, bawai maganar takarar shugaban kasa ba ce, aiki ne yake kaishi.