fbpx
Monday, May 16
Shadow

Duk Labarai

An kashe ɗaruruwan ƴan Boko Haram a Tafkin Chadi

An kashe ɗaruruwan ƴan Boko Haram a Tafkin Chadi

Tsaro
Aƙalla mayaƙan Boko Haram 300 aka kashe a yankin Tafkin Chadi a farmakin da dakarun hadin guiwa na rundunar MNJTF suka kai. Dakarun MNJTF sun ƙunshi na Kamaru Chadi da nijar da Najeriya da Benin. Jaridar ƙasar Chadi mai zaman kanta ta Tchad Infos ambato kakakin rundunar Kamaudeen Adegoke yana cewa an kashe mayakan na Boko Haram ne a farmaki 30 da aka kai masu a makwannin baya bayan nan. Ya ƙara da cewa mayaƙa sama da 52,000 da iyalansu suka miƙa wuya ga rundunar MNJTF.
Da Duminsa:EFCC ta kama babban akawu na kasa saboda bacewar Naira Biliyan 80

Da Duminsa:EFCC ta kama babban akawu na kasa saboda bacewar Naira Biliyan 80

Siyasa
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama babban akawun Najeriya, Ahmad Idris da ake zargi kan aikata ba daidai ba da Naira Biliyan 80.   An kama shine a Kano inda kuma tuni an zarce dashi zuwa Abuja.     The Economic and Financial Crimes Commision has arrested the Accountant General of the Federation, Mr. Ahmed Idris, over alleged mismanagement of N80billion, THISDAY has learnt. Sources said the arrest was made in Kano and he was currently being moved to Abuja. The commission is expected to issue a statement shortly.
Kalli hotunan gawarwakin ‘yan IPOB 4 da sojojin Najeriya suka kashe a yau

Kalli hotunan gawarwakin ‘yan IPOB 4 da sojojin Najeriya suka kashe a yau

Tsaro
FOUR IPOB/ESN ELEMENTS MEET THEIR WATERLOO IN FIERCE ENCOUNTER WITH TROOPS …The terrorists were taken out today Monday 16 May 2022, while shooting sporadically, threatening lives and property of innocent citizens.   Items recovered from the encounter, include one pump action short gun, 10 live cartridges, one Hilux truck, which was reportedly, snatched at gun point, yesterday by the irredentists, mobile handsets and charms.   Members of the public are please enjoined to provide credible information on the movement of the criminal elements to security agencies, whenever sighted in their communities. https://twitter.com/HQNigerianArmy/status/1526278767441858566?t=tgntSsx3r3ENnT8mbAbb1A&s=19  
Kotu ta tura mutum biyar gidan yari a Edo kan laifin zamba ta intanet

Kotu ta tura mutum biyar gidan yari a Edo kan laifin zamba ta intanet

Uncategorized
Wata kotu a Jihar Edo ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin Benin. Tun daga farko hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa wato EFCC ce ta kai mutanen ƙara bisa zarginsu da amfani da intanet wurin aikata zamba cikin aminci. Waɗanda aka aika gidan yarin sun haɗa da Amogie Julius da Omogbon Friday Harry da Osaze Okoro da Lucky Tegiri da kuma Omokhua Destiny. Duka waɗanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa inda cikin laifukan har da batun yin sojan gona ga jam'ian ƙasashen waje da zummar yin zamba ga jama'a don karɓar musu kuɗaɗen su.
Hotunan zakakuran matasan lauyoyi da suka kare wanda ake zargi da kashe Deborah Sokoto

Hotunan zakakuran matasan lauyoyi da suka kare wanda ake zargi da kashe Deborah Sokoto

Uncategorized
LAUYOYI MUSULMI: Wadannan sune zaratan Lauyoyi Musulmai da suka tsaya a Kotu domin ganin sun kare Matasan da aka kama bisa zargin k@$he Deborah (L) wadda tayi batanci ga Annabi Muhammad SAW a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake Sokoto. Muryoyi ta samu rahoto daga Mujallar Sokoto da ta wallafa cewa Lauyoyin na karkashin jagorancin wani Barista Mustapha Abubakar Mada sun nemi Kotu da ta bayar da belin Matasan sai dai Kotun ta dage Shari'ar har zuwa ranar Laraba 18/05/2022 domin duba bukatar belin nasu. Jaridar ta ruwaito ana tuhumar Matasan ne da laifin hadin-kai wajen cin amana (Criminal Conspiracy) da kuma zuga Jama'a wajen tashin hankali (Inciting Public Disturbance). Me zaku ce?
TURKASHI: Budurwa Ta Maka Mahaifinta A Kotu A Jihar Kaduna Saboda Ya Hana Ta Auren Wanda Take So

TURKASHI: Budurwa Ta Maka Mahaifinta A Kotu A Jihar Kaduna Saboda Ya Hana Ta Auren Wanda Take So

Uncategorized
Daga Sani Musa Mairiga Tirkashi, so hana ganin laifi! Wata budurwa mai karancin shekaru mai suna Halima Yunusa ta maka mahaifinta a kotun shari'ar musulunci dake Magajin Gari a jihar Kaduna, saboda wai ya hana ta auren wanda take matukar so, wato Bashir Yusuf Yunusa wanda ke zaune a Kasuwar Magani dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna. Ta shedewa kotun cewa tana matukar kaunar Bashir amma iyayenta sun ce faufau ba za su taba yarda ta aure shi ba. Shine dalilin da ya sa ta yi karar mahaifin nata. Malam Ibrahim wanda shine mahaifin budurwar ya shedewa kotun cewa yana sane da soyayyar dake tsakanin 'yar sa da saurayin wanda har ya umurce shi da ya turo iyayen sa su kawo sadaki amma shuru kake ji yau kusan shekara daya kenan.
Kotu Ta Tura Wadanda Ake Zargi Da Kashe Deborah Gidan Yari

Kotu Ta Tura Wadanda Ake Zargi Da Kashe Deborah Gidan Yari

Uncategorized
Daga Aliyu Samba Rundunar ‘yan sanda ta jihar Sakkwato ta gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan daliba mai matakin aji na 2 a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, Deborah Samuel da ake zargi da furta kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama cikin wani sakon sautin murya a dandalin sada zumunta na whatsapp. Wadanda ake zargin, Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunchi wadanda suma daliban kwalejin ne, an gurfanar da su a gaban wata kotun majistare da ke jihar Sakkwato a ranar Litinin. A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya sakamakon harin da suka yi wanda ya kai ga halaka dalibar. Bayan wadanda ake zargin sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, dan sanda mai shigar da kara, In...