fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Duk Labarai

Alkali ya kashe auren wani mutum sannan ya aure matar daga baya

Alkali ya kashe auren wani mutum sannan ya aure matar daga baya

Uncategorized
Jihar Legas ta sauke wani alkali me suna Mr Ishola Razaki Adeyemi Daga mukaminsa bayan da ya kashe auren wani mutum, Adeyemi sannan ya kwace matar.   Adeyemi yace bayan ds ya tunkari alkalin kan maganar, yasa an kamashi aka daure.   Sannan kuma aka kaishi gidan yarin kiri-kiri. Ya kuma kara da cewa, ya hanashi ganin 'ya'yanshi.   A karshe dai an sauke alkalin daga mukaminsa.
Duk shekara, gwamnati na ware biliyan 1 dan tallafawa ‘yan Najariya>>Minista Sadiya

Duk shekara, gwamnati na ware biliyan 1 dan tallafawa ‘yan Najariya>>Minista Sadiya

Siyasa
Ministar kula da ibtila'i da jin kai, Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya na ware biliyan 1 duk shekara dan tallafawa marasa karfi.   Tace ana ware kudinne a karkashin tsarin NSIP. Ta bayyana hakane a Osgbo dake jihar Osun wajan kaddamar da shirin tallafawa gajiyayyu.   Jami'in ma'aikatarta, Mr Nasir Gwarzoh da ya wakilceta a wajan taron ya bayyana haka.   Yace gidaje Miliyan 12 ne suka amfana da lamarin.
Maganar maja tsakanin NNPP da Labour Party ta mutu murus tun tuni, cewar babban darektan Peter Obi

Maganar maja tsakanin NNPP da Labour Party ta mutu murus tun tuni, cewar babban darektan Peter Obi

Siyasa
Babban darektan kungiyar dake yiwa Peter Obi yakin neman zabe, Doyin Okupe ya bayyana cewa maganar maja tsakanin NNPP da Labour Party ta mutu makonni hudu da suka gabata. Inda yace Kwankwaso yana so yayi amfani da farin jinin Obi ne don yayi nasarar lashe zaben shekarar 2023. Saboda haka su sun janye ra'ayi akan hakan tun tuni amma NNPP ne suke cigaba da matsa masu akan maganar domin suyi amfai da Obi. Ya bayyana hakan ne yayin daya ke ganawa da Channels inda yace basu sanar da hakan a kafafen sada zumunta bane saboda sanin ya kamata.
Ji bayani dalla-dalla yanda ‘yan Bindiga suka kaiwa tawagar motocin shugaba Buhari hari

Ji bayani dalla-dalla yanda ‘yan Bindiga suka kaiwa tawagar motocin shugaba Buhari hari

Uncategorized
Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta da bacin ranta kan wani hari da aka kai wa ayarin motocin Shugaba Muhammadu Buhari a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsina. Wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar ta ce an kai harin ne kan ayarin motoci dauke da jami'an da ke wa shugaban hidima yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Daura gabanin bikin Babbar Sallah. Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ba ya cikin ayarin motocin. Garba Shehu ya kara da cewa wasu mahara da ba a tantance ko su wane ne ba sun yi wa ayarin wuta kwanton-bauna, kuma sun bude wa jami'an wuta. Sai dai sanarwar ta ce jami'an da ke tsaron lafiyar shugaban kasa sun yi nasarar kare kansu kuma sun kora maharan. Cikin jami'an tsaron akwai 'yan sanda da ...
‘Yan bindiga sun kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina

Tsaro
'Yan bindiga sun kashe kwamishinan hukumar 'yan sanda na yankin Dutsinma a jihar Katsina, ACP Aminu Umar tare wani jami'i guda a karamar hukumar Safana. 'Yan bindigar sun kashe sune a wani harin kwantan bauna da suka kaiwa hukumar. Mai magana da yawun hukumar na jihar Katsina, Gambo Isa ya tabbatar da wannan rahoton inda yace 'yan bindigar su kusan 300 suka zo akan babura. Kuma sunyi nasarar kashe masu jami'an ne yayin da suke musayar wuta a daren jiya da misalin karfe 11:30 na dare.
Ko ana ha maza ha mata Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba a shekarar 2023, cewar tsohon shugaban hukumar Delta

Ko ana ha maza ha mata Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba a shekarar 2023, cewar tsohon shugaban hukumar Delta

Siyasa
Tsohon shugaban hukuma agaji mai zaman kanta a jihar Delta, Asari Dokubo ya bayyana cewa Peter Obi ba zai taba zama shugaban Najeriya ba a shekarar 2023. Dokubo yace Obi makaryaci ne kuma mayaudari saboda haka ba zai taba maye gurbin Buhari a Villa ba shekarar 2023. Kuma yace ba zai taba yiyuwa a danganta shi da Atiku Abubakar na PDP ba ko kuma Bola Tinubu na APC domin duk doke ahi zasuyi. A karshe yace babu abinda Obi ya tsinanawa jihar Anambra a shekaru takwas da yayi a lokacin da yake gwamna.
Don Allah ka dauki mace a matsayin abokiyar takararka, matan APC suka roki Tinubu

Don Allah ka dauki mace a matsayin abokiyar takararka, matan APC suka roki Tinubu

Siyasa
Kungiyar masoyan Tinubu ta mata ta bukaci dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC cewa ya zabi mace a matsayin abokin takararsa. Inda suka bayyana cewa mata da dama a jam'iyyar APC suna son Tinubu ya mulki Najeriya domin zai kawo sauyi. Shugabar kungiyar, Bolanle Kazeem ce ta bayyana hakan a babban birnin tarayya yayin da suke zagaye suna wayar da kan mata suyi katin zabe. Inda tace Tinubu zai kawo sauyi a kasa sosai ta fannin matsalar tsaro da cai sauransu kamar yadda yayi a jihar Legas.
‘Yan bindiga sun kashe dan sanda sunyi garkuwa da dan kasar Sin a jihar Kwara

‘Yan bindiga sun kashe dan sanda sunyi garkuwa da dan kasar Sin a jihar Kwara

Tsaro
'Yan bindiga sunyi garkuwa da wani dan kasar sin kuma sun kashe jami'in dan sanda a harin da suka kai karamar hukumar Moro a jihar Kwara. 'Yan bindigar sun babbaka motar hukumar kafin daga bisani suka tsere, kuma sun jigata wani jami'in wanda yanzu yake jinya a asbiti. Mai magana da yawun hukumar na jihar, Okasanmi Ajayi ne ya tabbatarwa manema labarai wannan labarin inda yace zasu tabbatar da cewa sun ceto dan kasar sin din. Kuma ya kara da cewa basu ji dadin kashe masu jami'i da aka yi ba sannan zasu kama wa'yanda suka aikata wannan laifin don a hukunt su.