Saturday, June 6
Shadow

Duk Labarai

Zaka tausayawa shugaba Buhari ka kuma jinjinamai bisa yanda ya tafiyar da harkar kasarnan daga lokacin daya hau mulki zuwa yanzu, bayan ka karanta wannan labarin

Zaka tausayawa shugaba Buhari ka kuma jinjinamai bisa yanda ya tafiyar da harkar kasarnan daga lokacin daya hau mulki zuwa yanzu, bayan ka karanta wannan labarin

Uncategorized
Kasancewar sayar da danyen man fetur babbar hanyar samun kudin shiga a Najeriya, yawancin lokuta ana alakanta cigaban da za'a samu da yawan kudin da kasar ta samu ta wannan hanya, jaridar The Sun tayi wani bincike daya fayyace yawan kudaden da gwamnatin Goodluck Jonathan ta PDP data gabata ta samu daga sayar da danyen man fetur da kuma yanda ta kashesu da kuma yawan kudin gwamtin shugaba Buhari ta samu itama daga danyen man fetur da kuma yanda ta kashe su. Idan aka kalli hoto na sama ya fayyace komai, kudin da Gwamnatin Buhari ta samu daga hawa mulki zuwa yanzu, watau watanni ashirin da bakwai, ko kuma muce shekaru biyu da wata uku Daga sayar da danyen man fetur, basu kai yawan kudin da gwamnatin Jonathan ta samu a shekara daya ba. Gaba dayan kudin da Gwamnatin Buhari ta samu sune d...
“Ba aikin ‘yan fim ne koyar da mutane tarbiyyaba”>>Sadiq Sani Sadiq

“Ba aikin ‘yan fim ne koyar da mutane tarbiyyaba”>>Sadiq Sani Sadiq

Uncategorized
A wata hira da yayi da bbchausa, Jarumin jaruman finafinan hausa, Sadiq Sani Sadiq ya tabo batutuwa da dama wadanda masoya finafinan hausa zasuso jinsu, daya daga cikin bayanan da Sadiq yayi shine cewa, bafa aikin 'yan fim bane koyawa mutane tarbiyya, ita tarbiyya daga gida ake samota, wasu masu sharhi akan harkokin finafinan hausa da dama sukanyi kushe akan yanda wasu 'yan fim ke taimakawa wajen lalacewar tarbiyyar jama'a, musamman matasa. To saidai a lokuta da dama wasu jaruman idan akayi hira dasu a gidajen watsa labarai sukan fadi cewa sufa suna fadakarwane, wasuma cewa suke wa'azi sukewa mutane akan wani abu wanda bashi da kyawu, amma koma dai menene shidai Sadiq ya fadi ra'ayinshi da kuma irin salon da yake ganin harkar fim take dauka. Sadiq din ya kuma bugi kirji inda yace shi...
Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara a 2019>>Fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara a 2019>>Fadar shugaban kasa

Uncategorized
Me magana da yawun shugban kasa, Garba Shehu ya bayyanawa manema labarai cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai iya tsayawa takarar shugabancin kasarnan a zabe me zuwa na shekarar 2019. Garba Shehu yace shugaban ya cancanci ya sake tsawa takarar lura da irin salon mulkinshi, kuma maganar rashin lafiyarshi, yace mutane da yawa basusan gaskiyar abinda ke faruwa da lafiyar shugaban kasa ba, amma dai abinda zai iya fadi shine shugaban yana da kuzarin da zai sake tsayawa takara. Amma Garba Shehu yaki yarda yayi magana akan ko wane irin ciwone yake damun shugaban kasar, yace idan shugaba Buhari ya dawo ya kuma ga cewa lokaci yayi dazai gayawa 'yan Najeriya irin ciwon dake damunshi to zaiyi hakan. Ya kuma kara da cewa ba shugaba Buhari bane shugaban kasa na farko daya fara yin rashin la...