fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Duk Labarai

Yanda masu zaman gidan kaso a kasar Isra’ila ke dabarar samun haihuwa da matansu ta barauniyar hanya

Uncategorized
A kasar Isra'ila akwai falasdinawa wanda aka yankewa hukuncin zama gidan kaso na tsawon shekaru saboda laifika daban-daban da suka aikata, masu iyali daga cikinsu na yin dabarar fitar da maniyyinsu ta barauniyar hanya dan kaiwa matansu dake can gida, a saka musu a mahaifarsu dan su samu su haihu. Kamar yanda wani me suna mustafa dake zaman gidan kaso yake gayawa wakilin Aljazeera a wata hira da yayi dashi. Ya kara da cewa wannan itace hanya daya tilo da zasu iya kasancewa da matansu ba tare da matan nasu sun manta dasu ba sun samu wasu mazajen sunyi aureba. Shi Mustafa yana da da namiji da matarshi me suna Maya ta haifa mishi ta irin wannan hanyar ta fitar da maniyyinshi ta barauniyar hanya, kuma an sakawa dan nashi suna Assad. Matar wani shima dake zaman gidan kason a kasar Isra'il...

Wata sananniyar me gabatarda shirye-shirye, Rachel ta ziyarci IBB: Sunsha hannu har sau biyu: Ta yabeshi sosai

Uncategorized
Wata sananniya me gabatar da shirye-shirye a kafafen watsa labari kuma 'yar rasjin kare hakkin bil'adama me suna Rachel Bakam ta kaiwa tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida(IBB) ziyara a gidanshi dake kan dutse a jihar Naija. Rachel ta wallafa wadannan hotunan a dandalinta da sada zumunta da muhawara inda ta bayya irin yanda tsohon shugaban yake birgeta saboda irin karamcinshi da kyawawan haleyenshi, da basira, da nutsuwa dake tattare dashi da kuma yanda yake sauraron mutane idan suna magana dashi, injita. Haka dai wannan baiwar Allah tayi ta zuga tsohon shugaban kasar, kuma tace ita da tawagarta sun mikawa IBB din wani katin godiya da gaisuwa haka kuma ta kara da cewa abinda ya kara birgeta shine irin yanda ya dauki lokaci ya karanta katin da suka kai mishi. Ha...

Wani Inyamuri daga jihar Imo ya musulunta: Ya zabi sunan ‘Yusuf’

Uncategorized
Wannan wani Inyamurine daga jihar Imo da Allah ya azurtashi da hasken zuciya ya amshi kalmar shahada jiya Juma'a kamar yanda wani wanda shima musulmin inyamurinne ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta da muhawara, shi dai wannan bawan Allah ya zabi sunan Yusuf bayan da ya yi kalmar shada. Muna mai fatan Allah ya kara fahimtar dashi addinin musulunci kuma ya karo mana irinsu. ko da a satin daya gabata an samu wata baiwar Allah me suna A'ishat Obi daga dai jihar ta Imo inda ta fito tace ina alfahari da kasancewata musulma , kuma ta karfafawa 'yan uwanta inyamurai gwiwa akan su fito su daina jin tsoron karbar addinin musulunci, kuma su tashi su nemi ilimin addinin.

Kalli yanda aka yiwa wannan gawar makara me siffar gida hada tauraron dan Adam

Uncategorized
Wannan hotunan wata gawace da aka mata makara me siffar gida hadda tauraron dan Adam, wadannan hotunan sun dauki hankulan mutane sosai musamman a dandalin sada zumunta da muhawara na yanar zigo, lallai Imani ma wani abune, Allah mun godema, ka kara shiryar damu akan hanya madaidaiciya. To amma dai wannan tabewar basira da yawa take kudin da suka kashe sukayi wannan makara, da abinci suka siya sai yafi musu amfani.   A cikin wadanda sukayi sharhi akan wannan hotunan wani yace, yana daya daga cikin abinda addinin musulunci ke birgeshi, irin yanda ake yin jana'izar mamaci cikin mutunci da sanin ya kamata.

Kalli kyawawan hotunan Nafisa Abdullahi: Tana kan hanyar dawowa Gida Najeriya daga Ingila

Uncategorized
Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar, ga dukkan alamu Nafisar dai na kan hanyar dawowa gida Najeriya daga kasar Ingila inda taje amso kyautar karramawa da aka mata tare da abokin aikinta Ramadan Booth. Bayan da Ali Nuhu ya musu jagoranci zuwa gurin amsar kyautukan da aka basu, jaruman sunje filin wasan kwallon kafa na kungiyar Chelsea watau Stamford Bridge inda suka kalli wasa tsakanin Chelsea da Manchester United kuru-kuru ba a kwalba ba, irin hotunan na suka wallafa a dandalinsu na shafukan sada zumunta da muhawara sun nuna yanda sukaji dadin hakan Daga nanne kuma da alama kowa ya kama gabanshi, domin ba'a sake ganin jaruman tare ba, ita Nafisa taje ziyara gurin sannanniyar gadar nan ta birnin Landan, sannan kuma ta shiga wani s...

Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari ta jewa tsohon gwamnan jihar Gombe, Goje ta’aziyyar rasuwar matarshi

Uncategorized
A yau Juma'ane uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari takai ziyarar ta'aziyya gidan tsohon gwamnan jiyar Gombe, Sanata Danjuma Goje bisa rasuwar matarshi marigayiya Hajiya Yelwa, a jiyane dai akayi jana'izar Hajiya Yelwa a garin Gombe. Muna fatan Allah ya jikanta yasa ta huta, idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da Imani.

Shugaba Buhari ya gana da malaman addini a fadarshi

Uncategorized
A yau Juma'ane shugaban kasa Muhammadu Buhari ga mataimakinshi farfesa Yemi Osinbajo tare da wasu ministoci suka gana da shuwagabanin addinan Musulunci dana kirista a fadar shugaban kasar, a lokacin ziyarar tasu shugaba Buhari yayi alkawarin gyara sukar da akewa gwamnatinshi na cewa ta bayar da mukamai ga 'yan Arewa fiye da 'yan kudu. Ya kara da cewa ya bayar da umarnin a kawomai sunayen shuwagabannin ma'aikatan dake rike da manyan ma'aikatun gwamnatin nashi dan ya duba yayi gayaran daya kamata. Haka shugaba Buhari yayi alkawarin ganin ya kula da bangaren shari'a da kuma jami'an tsaro dan ganin an samu zaman lafiya me dorewa a kasarnan.

Shawarwarin rayuwa daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Uncategorized
SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Don Allah kada a hada kai da kai a zalunci wani. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Ka yi aikin kirki, domin duniya ba matabbata ba ce. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Ka tsaya a kan gaskiya, duk rintsi duk wahala. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ In ka ga wasu suna husuma, yi iya bakin qoqarinka ka sasanta, sai dai  in abin ya fi qarfinka. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Ka guji hassada, domin bayan haddasa gaba dazatayi tsakanin ka da dan'uwanka, zata kuma cinye ayyukan ka. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Ka rike girmanka da Allah ya ba ka, domin ba dabaranka ne yakawo maka girman ba. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Kadauki na sama dakai a matsayin iyayenka, sa'anninka a matsayin abokanka, na kasa dakai a matsayin 'ya'yanka. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Shiga haqqin mutane ba shi dakyau, Allaah ne Ya hana, ka guji yin hakan, domin zai kaika ga halaka. SHAWARA CEπŸ‘ŒπŸ½ Kada kayi don ka faran