fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Duk Labarai

Sule Lamido ya kaiwa Muhammad Indimi ziyara a ofishinshi dake Abuja

Sule Lamido ya kaiwa Muhammad Indimi ziyara a ofishinshi dake Abuja

Uncategorized
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido kuma me neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, karkashin tutar jam'iyyar PDP, ya kaiwa hanshakin attajirin dan kasuwa kuma sirikin shugaban kasa Muhammad Indimi ziyara a Ofishinshi dake Abuja jiya Juma'a.  sun tattauna batutuwa daban-daban a Ofishin na Muhammad Indimi, kuma an hango mijin diyar shugaban kasa, wanda dama dane a gurin Muhammad Indimin watau Ahmad Indimi cikin tawagar baban nashi. Muna musu fatan Alheri.
An yiwa Maryam Gidado nadin Sarautar “Inna Wuron” Kannywood

An yiwa Maryam Gidado nadin Sarautar “Inna Wuron” Kannywood

Uncategorized
Kungiyar masu shirya fina-finai na Arewa reshen jihar Zamfara sun yiwa tauraruwar fina-finan Hausar Maryam Gidado nadin sarautar " Inna Wuron" masana'antar finafinan Hausa ta Kannywood, an sakawa Maryam Alkyabba sannan aka bata sandar Sarauta haka kuma aka sakamata Malafa. Haka kuma an yiwa Abdullahi Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Baba karami nadin Sarauta shima a gurin, amma ya zuwa yanzu bamu san kowace sarautace aka nadashiba amma da zarar mun samu bayani zamu sanar daku in Allah ya yarda. Muna taya Maryam da Baba karami Murna da fatan Allah ya kara daukaka.
Bbchausa tayi hira da Ali Nuhu da Ramadan Booth

Bbchausa tayi hira da Ali Nuhu da Ramadan Booth

Uncategorized
A jiya Juma'a ne kafar watsa labarai ta bbchausa tayi hira da jaruman finafinan Hausa, Ali Nuhu(Sarki) da Ramadan Booth wadanda yanzu haka suke can kasar Ingila dan halartar kayataccen taron karrama jaruman fina-finan nahiyar Afrika da wata mujalla me suna African Voice ke shiryawa, a wannan shekarar Ramadan Booth dinne zai amshi kyautar karramawa ta jarumin jarumai na masana'antar Kannywood. A yau Asabar ne za'a bayar da wannan kyauta In Allah ya yarda, muna taya Ramadan Booth murna da fatan Allah ya kara daukaka
A Gobe Kanal Abu Ali Zai Cika Shekara Guda Da ‘Yan Boko Haram Suka Kashe Shi A Fagen Daga: Iyalanshi zasu yimai addu’a ta musamman

A Gobe Kanal Abu Ali Zai Cika Shekara Guda Da ‘Yan Boko Haram Suka Kashe Shi A Fagen Daga: Iyalanshi zasu yimai addu’a ta musamman

Uncategorized
Wanene Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali? Labarin rasuwar kwamandan rundunar sojin Nijeriya ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali, shi ne kusan batun da ya fi kowanne jan hankalin ma'abota shafukan sada zumunta a Nijeriya a ranakun karshen mako. Laftanal Kanal Abu Ali yana cikin sojoji biyar da suka rasa rayukansu a daren Juma'a, yayin bata kashi da mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai hari kan wani barikin soji dake Mallam Fatori a jihar Borno. Rundunar sojojin Nijeriyar ta sha bayyana dakarunta da su ke rasa rayukansu a rikicin Boko Haram, a matsayin jarumai, wadanda suka sadaukar da rayukansu don kare rayukan sauran jama'ar kasar. Sai dai a wurin hukumomin sojin Nijeriyar, jarumtar Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali ta daban ce. Hakan ne ma ya sa ya sa...
“Kada wanda ya kirani da ranka ya dade”>>inji Sabon sakataren gwamnatin tarayya

“Kada wanda ya kirani da ranka ya dade”>>inji Sabon sakataren gwamnatin tarayya

Uncategorized
A ranar larabar data gabatane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon sakataren gwamnati, Boss Mustafa bayan da ya kori  Babahir daga aiki, bayan rantsar dashi dinne kuma sakatare me rikon kwarya ya mika takardun aiki, Boss Mustafa ya bukaci kada wanda ya kirashi da ranka ya dade/mafifici/megirma, ya kara da cewa baisan daga inda mutane suka samo wannan kalmaba domin dai kundin tsarin mulkin kasa da muke amfani dashi bai ambacetaba. Ya kara da cewa koda kalmar shuga me cikakken iko da ake gayawa gwamnoni babu ta a tsarin milkin kasarnan, abin da tsarin mulki ya kira gwamna shine gwamnan jiha kaza kawai. Saboda haka ya roki duk wanda zai kirashi ko kuma zai ambaceshi a wani guri to yace mai sakataren gwamnatin tarayya kawai, domin kamar yanda yace shi baifi kowane mutu...
Atiku ya musanta labarin dake cewa wai bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zabe me zuwa

Atiku ya musanta labarin dake cewa wai bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zabe me zuwa

Uncategorized
Tsohon mataimakin shugaban kasa, wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ya musanta labarin da ake yadawa cewa wai ya bayyana aniyarshi ta tsayawa neman takarar shugbancin kasarnan a zaben shekarar 2019, wasu kafafen watsa labarai sun bayyana cewa sun samu lalabarin Atikun yayi magana akan tsayawarshi takarar a 2019 amma ya fito a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter ya karyata wannan lamari. Atikun dai yaci karo da irin wannan labarinne da wata sanniyar kafar watsa labarai ta wallafa inda ya tambayi cewa "wannan labarin karyar yanata watsuwa a kafafen watsa labarai da dama, ina mamakin wanene ya aika musu dashi(Murmusi)" Duk da ya karyata wannan labarin wasu masoyanshi sunce su sun kagara dama ya fito ya bayyana wannan aniya tashi saboda haka su kam sunji dadin ...