1- MAINENE HUKUNCIN TA A MUSULUNCI?
WABIJINE KOWA YAYI WANNAN ZAKKAR,
SABODA HADISIN IBN ABBAS, DA BIN UMAR RA. MANZON ALLAH SAW, YA WAJABTA WANNAN ZAKKA , AKAN DUKKAN MUSULMI, NAMIJI DA MACE, DA, DA BAWA ,BABBA DA YARO,
BUKHARI DA MUSLUM,
2- MAINENE HIKMAR WANNAN ZAKKA?
MALAMAI SUNYI MAGANGANU , GAMAI DA HIKMAR WANNAN ZAKKA,
NA DAYA : DOMIN GODIYA GA ALLAH AN GAMA AZUMI LAFIYA,
NA BIYU: DOMIN FARANTAWA TALAKAWA, RANAR SALLAH, SU SAMI ABIN YIN TUWON SALLAH,
NA UKU: DOMIN SAMUN GAFARAR ALLAH GAMAI DA KURAKURE DA AKA AIKATA A CIKIN RAMADANA.
NA HUDU: ZAKKA CE DA AKE FITARWA ,DOMIN GODIYA GA ALLAH, DAYA RAYA KA HAR ZUWA SHEKARA, WASU DA
YAWA SUN MUTU KAFIN.
NA BIYAR: SAMUN LADA MAI YAWA, DA CIKE GURMIN INDA AKA SAMI TAWAYA A CIKIN AZUMI.
NA SHIDA: KOYI DA ANNABI WAJAN CIYARWA GA TALAKAWA...