fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Duk Labarai

Dino Melaye cikin motarshi ta alfarma

Dino Melaye cikin motarshi ta alfarma

Uncategorized
Sanata Dino Melaye kenan, wanda ya fito daga jihar Kogi a cikin daya daga cikin rantsatssun motocinshi na alfarma da yake takama dasu, mutane da dama dai suna Allah wadai da irin yanda yake nuna rayuwar kece raini, suna ganin cewa kudin talakawane yake amfani dasu wajen siyan irin wadannan motoci, wasu kuma na ganin cewa a matsayinshi na Uba, me fada aji da kuma shekarunshi, ya wuce ace yana irin wannan fankama, amma da alama shi ko a jikinshi.

Karanta yanda TASHEE ya samo asali

Uncategorized
Tashe yana daya daga cikin al'adun Hausawa na asali kuma ana yinsa ne a cikin watan azumin Ramadan. Shugaban Sashen Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Malam Yusuf Muhammad, ya ce kalmar tashe ta samo asali ne daga kalmar tashi wato tashi domin sahur yayin daukar azumi. "Wasannin tashe sun samo asali ne daga Nalako, wanda sarki ne yake nada shi wato a matsayin sarkin gwagware - wadanda suka dade ba su yi aure ba," in ji shi. Nalako yana kewayawa ne yana wasanni don tashin gwagware daga bacci saboda ba su da matan da za su rika tashinsu. Har ila yau, ya ce tashe yana taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihin Hausawa, kodayake, ya ce zamani ya fara yin tasiri ga al'adar. bbchausa.

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA IYAYE MASU BARIN ‘YA’YAN SU MATA ZUWA TAHAJJ

Uncategorized
Muna kira da baiwa iyaye shawara a kan 'ya'yan su mata. Lokacin Sallar Dare ya yi, lokacin ne mata suke da cikakken 'yanci tun daga karfe goman dare har zuwa karfe hudun Asuba. Lokacin ne wasu daga cikin 'batagarin mata suke haduwa da 'batagarin maza domin yin shashanci. Iyaye kun turo 'yar ku wajen Sallah, amma ta tafi wajen saurayin ta. Ina baiwa iyaye shawara da su sa ido ainun a kan 'ya'yan su mata lokacin tafiyar su Sallar Tahajjud, inda hali a hada su da wani yaro ko yarinya masu wayo su tafi sallar tare. Domin wallahi akwai matan da ba sallar suke zuwa ba, kawai sheke ayar su suke yi da samarin su. Za ka ga yarinya ta taho wajen wa'azi ko sallar, amma ta tsaya ko ta tafi wajen samarin ta suna fira cikin dare. Su kuma Hukuma tun daga kan 'Yan Sanda, "Civil Depence", kwamitin Sha...
Kalli wata irin kwalliya

Kalli wata irin kwalliya

Uncategorized
Jarumar Fim din hausa, Maryam gidado kenan da wata irin kwalliya a gefen Ido. Da ala kuma ba ita kadai.ta fara yin irin wannan kwalliyar ba, domin abokiyar aikinta Sadiya Kabala itama ta fito da wata irin salon kwalliya data so tayi shige da tata. Saidai ta sa'adiya kabala a kumatune kuma kamar zanene. Ko irin wannan kwalliyar zata samu karbuwa gurin 'yan mata kuwa?.