fbpx
Friday, December 2
Shadow

Duk Labarai

Ana biyan Ronaldo miliyan dari da ashirin da shida akan kowane hoto daya saka a shafin Instagram

Uncategorized
Wani rahoton da jaridar Daily Mail ta kasar Ingila ta buga yace tauraron kwallon kafa dan kasar Portugal me bugawa kungiyar Real Madrid wasa, Cristiano Ronaldo ne dan kwallo daya tilo dake cikin mutane goma na farko da ake biya mafi yawan kudi a duk lokacin da suka saka wani hoto a dandalinsu na shafin Instagram. Rahoton yace a kowanne hoto da Ronaldo ke sakawa a dandalin nashi na Instagram ana biyanshi zunzurutun kudi Euro 310,000, wanda daidai yake da kudin Najeriya naira miliyan dari da ashirin da shida. Ana biyan Ronaldo wadannan kudine saboda yawan mabiya da yake dasu a shafin suka kai miliyan dari da shida kuma shine mutum na uku mafi yawan karbar kudi da mabiya, yana bin bayan Selena Gomez da Kim Kardashian. Mafi yawancin hotunan da Ronaldo yake sakawa na wuraren yawan shakata...

Kotu taci tarar mutumin daya saci miliyan dari biyu tarar dubu dari

Uncategorized
Wannan wani tsohon manajan bankin Skye bank ne me suna Tajudeen yusuf da hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa(EFCC) ta kama da laifin yin zamba cikin aminci, inda yayi sama da fadi da zunzurutun kudi naira miliyan daribiyu na wani mutum dake hulda da bankin da yake aiki dashi, shidai mutumin ya kawowa Tajudeen kudinne dan a saka mishi a asusun ajiyarshi dake bankin amma sai Tajudeen ya baiwa mutumin(mekudin) takardar alamar cewa an sakamai kudin a asusun ajiyarshi na bogi, sannan ya karkatar da kudin dan yin amfanin kanshi dasu. Kuma duk wani kokari da akayi na kwato kudin a hannun Tajudeen yaci tura, wannan yasa aka garzaya dashi babban kotun garin Jos. Kamar yanda kafar yada labari ta Premium Times ta ruwaito an tuhumi tajudeen da laifuka biyar da suka shafi zamba ci...
Anyi ce-ce-kuce akan wannan kwalliyar ta A’isha Tsamiya

Anyi ce-ce-kuce akan wannan kwalliyar ta A’isha Tsamiya

Uncategorized
Bayan saka wannan hoton a data sha kwalliya irinta zamani a shafinta na sada zumunta da muhawara, jarumar fim din hausa,  A'isha Tsamiya ta samu ra'ayoyi danban-daban akan hoton, wasu sun yaba da hoton inda sukace kwalliyar tayimata kyau, amma wasu da yawa kuma sun kushe wannan kwalliya inda sukace irin wannan kwalliyar tayi yawa kuma bata dace da Jaruma kamar A'isha Tsamiyaba, ainihin fukarta wadda babu kwalliya tafi kyau, kamar yanda da dama daga cikinsu suka bayyana. Gadai hotunan ra'ayoyin da mutane suka rubuta: Karin hotuna.
Yaushe Ali Nuhu zai daina rawa da waka a fim?

Yaushe Ali Nuhu zai daina rawa da waka a fim?

Uncategorized
Fitaccen mai shirya fina-finan Hausa Ali Nuhu Mohammed yace zai daina rawa da waka a fina-finan Hausa idan lokaci ya yi. Jarumin mai kuma shirya fina-finan na Hausa ya ce yana yin rawar da waka ne kawai idan akwai bukatar haka a cikin fim. Ya ce a yanzu ya rage yawan rawa da yake yi a fina-finan idan aka kwatanta da baya. Ali Nuhu ya ce a matsayinsa na jarumi, yanayi ne ya ke sa shi yin rawa a cikin fim din Hausa. Ya kara da cewa zai daina rawa da waka idan lokacin da ya kamata ya daina ya yi, to sai dai bai bayyana ko wane lokaci ne zai daina rawar ba. A kwanan nan ne dai Ali Nuhu ya fara nuna wani fim mai suna Mansoor a gidajen Kallo, fim din da ake ga ya kawo sauyi a harkar fina-finan Hausa. bbchausa.
Karin bayani kan gasar da Adam A.Zango ya saka

Karin bayani kan gasar da Adam A.Zango ya saka

Uncategorized
A jiyane shafin hutudole.com ya kawomuku labarin cewa jarumin fim din hausa kuma mawaki , Adam A. Zango ya saka wata gasa akan wakar fim dinshi da yake shiryawa na Gwaska, to saidai da alama wasu basu fahimci yanda gasar zata kasance ba, kuma haka yasa Adamu ya kara yin bayani akan wannan gasa daya saka kamar haka: "Wannan itace wakar da Adam A. Zango ya saka gasa a kanta. Maza zasuyi mata group dance duk wadanda sukazo na 1 suna da kyautar Naira dubu dari da hamsin da kuma rigar gwaska Na biyu kuma sunada kyautar naira dubu 100 da T-shirt na gwaska wadanda sukazo na uku kuma suna da kyautar naira dubu hamsin. mata kuma zasuyi miming din wakar cikin shaukin soyayya duk wadda tazo na 1 tanada kyautar waya da kuma atamfa 3, material 3 da kuma gyale 3. Ta 2 kuma tanada kyautar karamar wa...
Burin Rahama Sadau ya cika:Priyanka Chopra ta kulata

Burin Rahama Sadau ya cika:Priyanka Chopra ta kulata

Uncategorized
Jarumar fim din hausa da aka dakatar, Rahama Sadau ta kara samun wani gagarumin cigaba a harkar sana'ar fim, domin kuwa burinta da ta dade tana mafarki yana daf da cika, kusan a koda yaushe akayi hira da ita a kafafen watsa labarai takan fadi cewa ita 'yar fim din datafiso kuma takeso ta zama kamarta itace, Priyanka Chopra, wato shahararriyar 'yar fim dinnan ta kasar Indiya. To ayaudai Hankalin Priyanka yakai kan wata magana da Rahamar tayi wadda take cewa "Saboda irin nasarar da Priyanka ta samu itama abin yana zaburar da ita domin ta zama kamar Priyankar", Rahama tayi wannan maganane a shafin sada zumunta kuma Prinyankar ta mayarmata da sakon inda tace "Nagode ina fatan haduwa dake nan bada jimawaba, ina miki fatan samun nasara a dukkan abubuwan da kikasa a gaba". Priyanka dai shaha...

Allah Sarki karanta irin kirarin Da Marigayi Danmasanin Kano Ke Yi Wa Allah A Wuraren Taro

Uncategorized
"BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM.GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI, MAI KOWA, MAI KOMAI, MAI YADDA YA SO, KAN WANDA YA SO, YAYIN DA YA SO, A INDA YA SO, KO ANA SO, KO BA A SO. GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI MAI BAWA KOWA KOMAI, BA SHIDA BUKATAR KOMAI A GURIN KOWA, KOWA KE DA BUKATAR KOMAI A GURINSA. MAMALLAKIN MAMALLAK, MAI BADA MULKI GA WANDA YASO, YA FUSGE DAGA WANDA YASO, YA DAUKAKI WANDA YASO, YA KASKANTAR DA WANDA YA SO, LILLAHI WAHIDIL KAHHARI. SARKIN DA BA SHI DA NAN, BALLANTANA YA YI NAN, BA SHI DA CAN, BALLANTANA YA YI CAN, A KO INA YANA NAN. NA FARKO NE BA DA FARAWA BA, NA KARSHE NE BA DA KAREWA BA, A BAYYANE YA KE BA A GANINSA, A BOYE YA KE BA DON BA YA NAN BA. SARKIN DA YA KASANCE TUN KAFIN KASANCE WA TA KASANCE, KUMA ZAI KASANCE BAYAN KASANCEWA TA ...
Yanda A’isha Tsamiya tayi murnar zagayowar ranar haihuwarta

Yanda A’isha Tsamiya tayi murnar zagayowar ranar haihuwarta

Uncategorized
Yanda jarumar fim.din hausa, A'isha Aliyu Tsamiya tayi murnar zagayowar ranar haihuwarta tare da abokan aikinta da masoya, anan matashin me shirya fim din hausa dinnan ne Abba me shadda yake ciyar da A'isha kek din da akayi dan murnar ranar, muna mata fatan Allah ya karo shekaru masu albarka amin. Karin hotuna. A karshe A'ihshata mika sakon godiya ga masoya da abokai da suka aikamata da sakonnin taya murna na wannan rana.