Jaruman fim din hausa da kuma suke haskakawa a fina finan turanci na kudancin kasarnan, Yakubu Muhammad da Rahama Sadau kenan a wannan hoton nasu da ya kayatar, muna musu fatan alheri.
Wannan labarin wata baiwar Allah ce me suna Sera Yusuf wadda ta tallafawa wasu yara masu yin bara da iyayensu, yaran suka daina bara suka koma makaranta sannan iyayen yaran suka samu sana'ar yi.
Sera ta kasance tana da shagon da take kasuwanci kuma kullun idan zata wuce bakin wata mahada tana ganin wasu yara guda biyu namiji da mace tana basu sadaka, da yaran suka lura da Sera na basu sadaka kullun sai suka nemi shagonta, wata rana tazo ta ajiye motarta zata shiga shago sai suka rugo suna rokonta "dan Allah ki bamu sadaka mu sayi abinci".
Koda Sera taga haka sai ta kirasu cikin shagonta tace musu tana so ita dasu su zama abokai, sukace mata sun yarda, ta tambayesu sunayensu yarinyar tace sunanta A'isha shi kuma yaron yace sunanshi Abdullahi, ta tambayesu shekarunsu A'isha shekararta ...
Shahararrun 'yan kwallon kafa musulmai kenan Demba ba dan asalin kasar Senegal da Abou Diaby dan asalin kasar Faransa da Jacque Faty wanda shima a Faransa aka haifeshi amma ya dawo bugawa kasar Senegal wasa, dukkan su a kasar Saudiyya sunje yin aikin Hajjin bana, Muna fatan Allah ya amsa ibadar dukkan alhazai ya kuma mayar dasu kasashensu lafiya.
Wannan wata tallar maganin berane da akeyi a garin Legas inda masu maganin sukayi amfani da sanarwar da fadar shugaban kasa suka ta bayar kan cewa beraye sun hana shugaba Buhari shiga Ofis dinshi wajan yin tallar, bayan hoton beran da kuke gani a jikin tallar an kuma rubuta da turanci cewa "sun kori shugaban kasa, kar ku bari kuma su koreku".
Wannan salo na tallar maganin bera jaha hankulan mutane a inda wasu abin ya basu dariya wasu kuma cewa sukayi wannan renine ga fadar shugaban kasar.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai yayin da Sarkin Lere Birgediya Janar Garba Mohammed (Mai Ritaya) ya kai wa gwamnan ziyara a fadar gwamnatin jihar ranar Talata a Kaduna.
bbchausa.
Duniya kenan kowa da irin kiwon daya karbeshi... wannan wata baiwar Allahce a garin Houston na jihar Texas dake kasar Amurka inda aka samu mummunar ambaliyar ruwa, a cikin kayanta kakaf babu wanda taga ya dace ta dauka sai karenta da suka saba, ta dorashi a wuya dan kar ya halaka.
Tawagar tsoffi jaruman fin din hausa da wandanda ake damawa dasu a yanzu karkashin jagorancin tsohuwar jaruma matar Sani Musa Danja, Zakin 'yan wasan Arewa wato Mansurah Isah suna zagayen duba marasa lafiya a asibitocin dake jihar Kano da kai musu kayan agaji.
Mansurah itace madugar wannan tafiya sannan tana tattara irin gudummuwar da mutane suka bayar karkashin wata gidauniya data kafa sai a kaiwa marasa marasa lafiya kayan agaji, wannan aikin alheri da sukeyi muna fatan Allah ya sakamusu da mafiyinshi.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi kenan a kasa me tsarki tare da 'ya 'yanshi zasu sauke farali, Muna fatan Allah ya amsawa alhazan bana ibadunsu ya kuma dawo dasu gida lafiya.
Innalillahi wa Inna ilahi raji'un, Allah ya yiwa tsohon dan majalisar dattijai, Sanata Kanti Bello rasuwa da safiyar yau a garin Abuja, shekarun Sanata kanti 72 a Duniya kuma yayi siyasa karkashin jam'iyayyar PDP, muna fatan Allah ya gafartamishi.
Fitacciyar jarumar fim din hausa, Jamila Umar, Nagudu ta zama meyiwa sabulun Sabil talla, jarumar dai na kara samun cigabane ta bangaren samun karbuwa gurin kamfanoni dake daukarta domin tayi musu tallar hajojinsu domin a yanzu haka Jamila tana yiwa kamfanin magi na Vedan talla kuma sai ga wannan, muna mata fatan alheri da kuma Allah ya kara daukaka.