fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Duk malamin da yace Na hana Sallah Allah ya Isa>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana bacin ransa kan malaman da ke cewa sun hana Salah.

 

Gwamnan yace malmai da suka san gaskiya, suna gani a Saudiyya, dakin Ka’aba da Masallacin annabi, Sallahu Alaihi Wasallam duka ba za’ayi Idi ba amma suna cewa an hana Sallah a Kaduna.

 

Gwamna yace ro Allah ya isar masu.

 

Yace kai idan akwai wanda zai fito yace ya dauki nauyin rantsuwar da suka yi na kare rayukan mutane shi a dora alhakin a kasan kuma malamai su ce za’a iya dauke wannan nauyi to zasu bude gari.

 

Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa babu Ranar Bude Kaduna sai randa suka ga lamura sun daidaita.

 

Yace akwai garuruwan da suka fara budewa amma ai sun ga sakamakon abinda ya faru.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *