Ya ce gwamnatin shugaba Buhari ita ce ummul abaisin dalilin da ya janyo kafuwar Kungiyar IPOB saboda salon mulkin nuna wariya da shugaba Buhari ke yiwa Inyamurai.
“Ina tabbatar muku a yau Idan Matasan Inyamurai suka dauki bindiga suka fara yakar kasar nan Nigeria sai ta zama tarihi, saboda Inyamurai sunanan ko ina a kasar nan” Inji tsohon Sarkin.
Ya kuma ce a yanzu Matasan Inyamurai basa shaawar komai gameda Nigeria Kai ko da batun zaben shugaban Kasa ma BA sa sonshi kawai su kasar su ta Biyafra su Ke so.
Madogara: Daily Times Nigeria