fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Duk shanuwar da muka gani a kan titin Akure zamu kamata – Gwamna Rotimi Aleredolu

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ce za a kama duk wata saniya da aka gani tana yawo a titunan Akure, babban birnin jihar.

A cewarsa, gwamnatinsa tana hana yin kiwo a cikin gari saboda gudun barke wa rikicin makiyaya da manoma ko mutanen gari.

Gwamnan ya fadi haka ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a kwanan nan, Inda yace mun dakarta yin kiwo a filin, na bada umurni idan mutane ko jami’an tsaro suka ga shanu yana yawo a kantiti su damke shi.

Ya kara da cewa ba zamu yadda su kawo mana rikici cikin gari ba, dole mu dakatar da su.

Wannan ya biyo bayan rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma a yankin Kudu maso Yamma, Inda gwamnonin yankin Kudu maso Yamma a ranar 25 ga Janairu, suka hana yin kiwo a fili ko a cikin gari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *