Ministar kula da ibtila’i da jin kai, Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya na ware biliyan 1 duk shekara dan tallafawa marasa karfi.
Tace ana ware kudinne a karkashin tsarin NSIP. Ta bayyana hakane a Osgbo dake jihar Osun wajan kaddamar da shirin tallafawa gajiyayyu.
Jami’in ma’aikatarta, Mr Nasir Gwarzoh da ya wakilceta a wajan taron ya bayyana haka.
Yace gidaje Miliyan 12 ne suka amfana da lamarin.