fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Duk dan takarar daya maye gurbin Buhari zai sha bakar wahala, cewar Peter Obi

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin tutar Labour Party, Peter Obi ya bayyana cewa duk shugaban kasar daya maye gurbin Muammadu Buhari a zaben 2023 zai sha bakar wahala.

Tsohon gwamnan Anambran ya bayyana hakan ne a jihar Legas ranar litinin a wani taro daya hakalatta na kungiyar LCCI.

Inda yace Muhammadu Buhari ya bata Najeriya sosai domin babu aikin yi a kasa kuma yara da yawa basa zuwa makaranta, sannan talauci ya yiwa mutane katutu sosai.

Wannan dalilin ne yasa duk wanda ya maye gurbinsa zai sha bakar wahala a zaben shekarar 2023.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.