Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ba ta taba sanya wata kungiya ko wani mutum da zai tattauna a madadin ta da ‘yan bindinga ba.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan a jiya, ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana tattaunawa da ‘yan bindinga a madadin gwamnati za a hukunta shi.
Kwamishinan a cikin wata sanarwa, mai taken ‘Babu wata tawaga da Gwamna El-Rufai ya nada don tattaunawa da yan bindinga, ‘ya ce: jita jita da ake yadawa a wasu kafafen watsa labarai na cewa Gwamnatin Jihar ta nada kwamitin tattauna da yan bindinga ba gaskiya bane.