Malam ya bada sako zuwa ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Fasto Mathew Hassan Kuka, da tsohon chief of staff na kasa akan idan har sun ce sai an baiwa Deborh hakkinta tabbas muma sai an bi mana hakkinmu akan kisan SARDAUNA DA TABAWA BALEWA DA yan Darikar Tijjaniyya 70 da aka kashe mana a Jos da mutane 700,000 da aka kashe mana filin idi a Jos, da kuma Yan uwa musulmi da aka kashe mana a garin Tabawa Balewa, muma duka sai an bi mana hakkin rayukan ‘yan uwanmu.
Malam ya kara da cewa duk sanda aka kashe musulmi a Nijeriya sai ka ji shugabanni sun yi shiru amma da an kashe wani ko wata wanda ba musulmi ba za ka ji kowa yayi chaa akai.
A karshe Malam ya yi kira ga Gwamnonin Arewa akan su tabbatar da shari’ar musulunci a jahohinsu, sannan ya yi kira ga al’ummar musulmin Nijeriya akan abzo ayi matsa daya ta musulmi mu dinga fitowa akan murya daya.