fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Duk wanda yasan ba zai iya samo Miliyan 100 ta sayen fom din takara ba, bai cancanci zama shugaban kasa ba>>APC

Kakakin jam’iyyar APC me mulki, Felix Morka ya bayyana cewa, duk wanda ba zai iya samar da Miliyan 100 na sayen fom din takarar shugaban kasa ba, bai kamata ya zama shugaban Najeriya ba.

 

Kudin sayen Fom din takarar shugaban kasa na APCn ya jawo cece-kuce musamman tsakanin ‘yan Najeriya inda da yawa ke cewa talaka ba zai iya zama shugaban Najeriya ba.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Silverbird.

 

Yace idan mutum bai da kudi, ya gayawa masu goyon bayansa abinda yake son yi, idan suna sonshi zasu iya tara mai wadannan kudi.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *