fbpx
Monday, August 8
Shadow

Duk wani gini da aka yi a filayen da ba su dace ba a Kano za mu rushe shi cikin kwana 100 idan muka kabi mulki a 2023>>Kakakin Abba Gida-Gida, Sabature

Duk wani gini da aka yi a filayen da ba su dace ba a Kano za mu rushe shi cikin kwana 100—Sabature

 

Kakakin dan takarar Gwamnan Kano a zaben 2019 da ya gabata, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar, idan Allah ya basu nasara a zaben Gwamnan Kano a shekarar 2023, a cikin kwana darin farko zasu rushe duk wani gini da aka yi a filayen da basu kamata ba.

 

Sakon da ya wallafa da turanci, Bature ya kara da cewa, za su cire dukkan sabbin Sarakunan da aka kirkiro a Kano, tare da dawo da Khalifa Muhammadu Sunusi II kan karagarsa a matsayin Sarkin Kano guda daya tilo.

Karanta wannan  Dan uwan Buhari daya yi barazanar rusa APC ya fice daga jam'iyyar

 

Kazalika ya ce “Ina tabbatar maku da cewa kwana darin farko zai kasance kwanakin Rusau ne a jihar Kano, inda za mu bi duk wani fili ko gini da aka yi ba bisa kaida ba za mu rushe shi” a cewarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.