(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A cewar shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus cikin jawabin da ya gabatar yau Juma’a a Geneva, babu shakka karancin mayanin mai sinadaran kariya daga cutuka masu yaduwa musamman ta fuskar shaka, zai haddasa babban tsaiko a yakin da ake da cutar ta Corona.
Cikin jawabin na Tedros Adhanom ya bayyana cewa a shirye suke su aike da kayakin karin bukata wajen kariya daga cutar ta Corona zuwa kasashen da suka bukaci hakan duk dai a wani mataki na hana ta yaduwa.
A cewar WHO ba kadai mayanin rufe hancin ne duniya ke kamfarsa ba, har ma da sauran kayakin da ke baiwa jiki kariya daga cutar inda ya sha alwashin umartar kamfanonin samar da kayakin gaggauta sarrafa wasu don baiwa al’umma kariya.
WHO ta bayyana cewa babban abin fargaba ne da tashin hankalin karancin mayanin da sauran kayakin kariya daga cutar wadda kawo yanzu babu rahoto kan wanda ya kamu da ita ya warke la’akari da yadda aka gaza kammala bincike kan maganinta har zuwa yanzu.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole