Gwamnonin Arewa sun koka da cewa Duniya ta ci gaba, dan haka bai kamata Fulani su rika daukar dabbobi zuwa guri-guri ba dan kiwo.
Gwamnonin sun yi maganane a karkashin kungiyarsu inda kuma suka nemi da gwamnatin tarayya ta tallafa musu kan yanda zasu samar da guraren kiwo na Zamani.
Hakanan sun kuma sha alwashin wayar da kan Fulanin Makiyaya kan daina daukar shanu zuwa gari-gari dan kiwo. Shugaban kungiyar Gwamnonin Simon Lalong ne ya jagoranci ganawar da suka yi.
Sun kuma yi Allah wadai da duk wani rikici dake faruwa.