Rahoton ta’addancin Duniya na shekarar 2017 da muke ciki wanda aka gabatar dashi yau Laraba a birnin Landan na kasar Ingila ya bayyana cewa an samu ragowar mutuwar mutane ta hanyar ta’addanci sosai cikin shekaru biyu a jere, rahoton yace wannan shekarar ta 2017 itace shekarar da ba’a samu mace-macen mutane da yawa ta hanyar ta’addanci ba idan aka kwatanta da sauran shekarun da suka gabata.
Da yake bayani akan Najeriya, Rahoton yace an samu raguwar mutuwar mutane sanadiyyar harin ta’addanci da kashi tamanin cikin dari a wannan shekarar da muke ciki.
Wannan ba karamin abin farin ciki bane, tsaro yana daya daga cikin abubuwan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali akanshi kuma gashi har Duniya ta shaida cewa an samu gagarumin cigaba.
muna fatan Allah ya karo mana zaman lafiya ya kuma taimaki shuwagabanninmu akan tsare-tsaren da suke dashi na Alheri ga talakawa.