fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ebonyi: An gurfanar da Wani Matashi A Gaban Kotu Bisa Zargin Yiwa Wata Mai Shekaru 20 Fyade

A ranar Litinin ne Aka gurfanar da wani Matashi mai shekaru 28, Chibueze Godwin a gaban wata Babbar Kotun dake jihar Ebonyi kan zargin yi wa yarinya ’yar shekara 20 fyade.

Godwin, wanda ake zargi da aikata laifin, sun kasance zaune gida daya tare da wadda ake zargi da  yiwa fyaden kamar yadda aka bayyanawa kotun a yayin sauraron karar.

Sai dai Wanda ake kara, Godwin ya musanta zargin da ake masa na aikata laifin a lokacinda ake tuhumar tasa.

Itama lauyan mai kara Misis Grace Chima ta bukaci kotu da ta hanzarta Nemawa wacca aka ci zarafi hakkin ta.

Daga bisani bayan sauraran duka bangarori biyun Mai shari’a Vincent Nwanchor, wanda ke jagorantar karar, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga Maris.

(NAN)

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.