Edinson Cavani yana shirin zama sabon dan wasan Manchester United na biyu a wannan kakar yayin da kuma zai ringa fuskantar takara daga wurin Anthony Martial a kungiyar, bayan United ta amince zata biya shi yuro miliyan 20.
Manchester United ta fara tattaunawa da tsohon dan wasan PSG da Napolin ne a cikin wannan makon bayan sun yanke shawarar cewa farashin da Dortmund ta sawa Jadon Sancho na yuro miliyan 107 yayi yawa.
A ranar sati jigajigan kungiyar Manchester United suka tabbatar da cewa yarjejeniyar su da Cavani tayi armashi kuma yanzu dan wasan zai saka hannu a takaddun kwantirakin shekaru biyu a United din.