Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, reshan jihar Ondo ta cafke wasu mutum 9 da laifin Dillancin tabar wiwi.
kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi Haruna Gagara shine ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar Edo.
A cewarsa hukumar tayi nasarar dakume wadanda ke da hannu cikin lamarin a sakamakon wani bayanan sirri da rundunar ta samu.
Wadanda ake zargi sun hada da Alex Moses, mai shekaru 35 sai Oshie Emmanuel mai shekaru 20; Friday Effiong, 31; Emmanuel Akpan, 25, da kuma David Friday, 19.