Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta kama Eberechukwu, matar tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Mrs Obiano, wacce ake bincike a kan zargin zamba, a halin yanzu tana hannun hukumar a Abuja.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce bai da masaniya kan kamun da aka yi wa matar tsohon shugaban kasar, ya kuma yi alkawarin gano bakin zaren tare da sanar da manema labarai halin da ake ciki.